Kafar yaɗa labarai ta BBC ta ce za ta ci gaba da bayar da rahotonnin da suka shafi Jamhuriyar Nijar duk da matakin da hukumomin ƙasar suka ɗauka na hana ɗaukar shirye-shiryensu.
A ranar Alhamis ne hukumomin Nijar suka sanar da dakatar da tasoshin rediyo na FM a faɗin ƙasar yaɗa labaran BBC har na tsawon wata uku.
Sai dai cikin wata sanarwa da BBC ta fitar ta ce duk da cewa matakin zai shafi ƙoƙarinta na kai wa ga ɗimbin masu sauraronta, hakan ba zai rage mata karfin gwiwa ba.
”Haƙika wannan mataki zai shafi ƙoƙarimu na kai wa ga masu sauraronmu da ke cike da bukatar samun labaranmu na gaskiya waɗanda ba su nuna ɓangaranci,” a cewar sanarwar daga ofishin hulɗa da jama’a na BBC.
“Muna kan ƙudirinmu na gudanar da aikin jarida bisa ƙwarewa, kuma za mu ci gaba da yaɗa labaran da suka shafi ƙasar ba tare da fargaba ko daɗaɗa wa wani ba.”