Cibiyar binciken kwakwaf ta kasa da ta tabbatar da dakile zamba a kasar nan, ta bayyana shirinta na ganin cewa ’yan siyasar da suke da takardun bogi a bangaren karatun su, ba za su sake tsayawa takara da takardun shaidar su ba.
Dr Iliyasu Gashinbaki, wanda shi ne shugaban cibiyar, ya bayyana hakan a lokacin wani taro da shugabannin kungiyar hada kan ja’iyyun siyasa ta IPAC ta kasa a Abuja ranar Talata.
Ya ce cibiyar za ta hada hannu da IPAC donmi taimakawa wajen tantance takardun masu neman takara tun kafin zaben fidda gwani a babban zaben 2027.
Shi ma da yake jawabi, Shugaban IPAC, kuma Shugaban kungiyar Allied People’s Movement na kasa, APM, Alhaji Yusuf Dantalle, ya ce, dole ne su dauki mataki na kawar da duk wasu ‘yan siyasa masu irin wannan burin a takardun bogi.
Ba za mu sake bari ƴan siyasa su tsaya takara da takardun bogi ba – Dr Gashin Baki
Date: