fidelitybank

Ba za mu kyale ‘yan Najeriya su shiga yakin Ukraine da Rasha ba – Gwamnati

Date:

Najeriya ta ce ba za ta ƙyale ‘yan kasarta su shiga cikin mayakan da ke yaki da Rasha a kasar Ukraine ba.

Wannan ya biyo bayan wasu rahotanni da ke cewa, an fara yi wa ‘yan kasar ‘yan sa kai rijista, domin su taimaka wa sojojin Ukraine a mamayar da Rasha ke yi wa kasar.

Ma’aikatar harkokin waje ta Najeriya ta ce, ofishin jakadanci Ukraine da ke kasar ya musanta taka wata rawa a wannan abin takaicin.

Sai dai ofishin jakadancin ya tabbatar cewa, wasu ‘yan Najeriya sun sanar da shi cewa a shirye suke a yi wannan yakin da su.

Ofishin jakadancin ya kuma nisanta kansa daga rahotannin da ke cewa, ya bukaci dukkan dan Najeriyar da ke son shiga yakin da ya biya dalar Amurka 1,000 a matsayin kudin tikitin jirgin sama da na biza.

Wannan matakin na Najeriya na zuwa ne bayan kwana daya da kasar Senega ta gargadi ‘yan kasarta masu sha’awar tafiya Ukraine da su guji daukan wannan matakin.

Ta umarci jakadan kasar Ukraine da ya sauke wasu bayanai da ofishinsa ya wallafa a Facebook yana kira ga ‘yan Senegal su yi rajista domin a tafi da su can su yi yaki. A rahoton BBC.

nigeria newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp