fidelitybank

Ba za mu kirawo Falasɗinawa da sunan ƴan ta’adda ba – BBC

Date:

BBC ta kare shawarar da ta yanke cewa ba za ta kira ‘yan ta-da-ƙayar-baya na Hamas da sunan ”yan ta’adda’ ba, a cikin rahotannin da take yaɗawa game da hare-haren baya-bayan nan a Isra’ila.

Wani mai magana da yawun BBC ya ankarar da cewa akwai daɗaɗɗen matsayi da tashar labaran ta duniya ta ɗauka cewa masu aika rahotanninta, ba za su yi amfani da sunan ‘yan ta’adda ba, su a kan kansu, sai dai fa idan suna ruwaito zancen wani.

Wani daɗaɗɗen wakilin BBC kan harkokin waje, John Simpson ya ce “kiran wani da sunan ɗan ta’adda, na nuna cewa, kana goyon bayan wani ɓangare ne a cikin lamari”.

Sakataren tsaron Birtaniya Grant Shapps ya ce wannan manufa na “daf da zubar da mutuncin”, tashar kuma akwai buƙatar BBC ta gano inda ta ajiye “tunaninta na sanin ya kamata”.

Mai magana da yawun BBC na cewa: “BBC tashar labarai ce mai zaman kanta ta fuskar tsarin gabatar da aikin jarida, wadda aikinta shi ne ta bayyana haƙiƙanin abin da ke faruwa ‘a ƙasa’ ta yadda masu bibiyarmu za su iya yanke hukunci da kansu.”

opra news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp