Jam’iyyar SDP mai adawa ta ce, ba za ta kalubalanci sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da hukumar zaɓe ta sanar ba wanda ya bai wa Bola Tinubu nasara.
Shugaban jam’iyyar Shehu Gabam, shi ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Abuja jiya Alhamis.
“Duk da cewa an samu kura-kurai a zaɓen, SDP ba za ta kalubalanci nasarar Tinubu ba na jam’iyyar APC a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa,” in ji Gabam.
Ya ce jam’iyyar ta yi na’am da zaɓin ‘yan ƙasa kuma sun amince da sakamakon zaɓen.