Shugaban ƙungiyar ma’aikatan jinya ta Najeriya, Morakinyo-Olajide Rilwan ya ce mambobinsu za su ci gaba da yajin aiki ne har sai gwamnatin ƙasar ta kammala biya musu manyan buƙatun da suka gabatar.
A ranar Laraba ne ƙungiyar ta fara yajin aikin gargaɗi na kwana bakwai a faɗin ƙasar, duk kuwa da ganawa da suka yi da ministan ƙwadagon ƙasar gabanin fara yain aikin.
Yayin wata hira da gidan talbijin na Channels, Rilwan ya ce ƙungiyarsa za ta rufe kunnuwanta daga kiraye-kirayen janye yajin aikin da ake yi mata matsawar ba a biya mata buƙatunta ba.
Buƙatun ma’aikatan jinyar dai sun haɗar da:
Gyara alawus ɗinsu na aikin dare.
Ƙara kuɗin alawus na tufafinsu na aiki.
Samar da tsarin albashi na musamman domin ma’aikatan jinya kawai.
Kara alawus na ƙarin ayyukan da suke yi bayan ainihin aikinsu.
Gwamnati ta ɗauki ma’aikatan jinya da yawa aiki domin rage karancin ma’aikata.
Gwamnati ta buɗe sashen ma’aikatan jinya a Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya domin kula da buƙatun aikin jinya kai tsaye.