fidelitybank

Ba za mu iya kammala aikin layin dogon dogon Rivers zuwa Borno ba – Gwamnati

Date:

Gwamantin tarayya ta ce, ba za ta iya kammala aikin shimfida layin dogo na jirgin ƙasa da ta ce, za ta yi da zai hada gabashin ƙasar da kudancin ƙasar ba, kafin ƙarewar wa’adin mulkin shugaban Muhammadu Buhari.

Gwamnatin ta ce kamala aikin shinfada layin dogon ba abu ne mai yiwuwa ba saboda ƙarancin kudaden da za’a yi aikin.

Ministan harkokin sufurin ƙasar Mu’azu Jaji Sambo ne ya sanar da hakan bayan kamala zaman majaslisar zartarwar ƙasar da ya gudana a ranar Laraba.

A cewar sa gwamnatin tarayyar, ba ta sami damar karbar kudin hadin guiwar da za’a gudanar da aikin ba, wanda hakan yasa suka gaza samar da kudaden da suka kamata a yi aikin.

Jihohin da za su ci gajiyar aikin sun haɗa da jihohin Ribas, Abia, Anambra, Imo, Ebonyi da Enugu, da Nasarawa, Benue, Plateau, Kaduna, Yobe, Borno, Bauchi da kuma Gombe.

Shekara biyu da suka gabata ne, tsohon ministan Sufurin Najeriya Rotimi Amaechi, ya ce, za a kamala aikin shimfida layin dogon na Fatakwal zuwa Maiduguri kafin karewar mulkin shugaba Buhari.

A lokacin kaddamar da shirin, an kiyasta cewa za a kashe kusan dala biliyan biyu wajen gina layin dogon, wanda suke cewar zai bunƙasa tattalin arzikin jihohin 14 da aikin zai shafa.

the punch newspaper today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp