Kungiyar kananan hukumomi ta kasa ALGON, ta ce, ba za ta iya biyan sabon mafi karancin albashi na Naira 62,000 ga ma’aikatan ta.
Kungiyar ta ALCON ta dora alhakin gazawarta wajen biyan kudaden da ake samu daga asusun tarayya da kuma wasu ayyuka.
Shugaban kungiyar ALGON na kasa, Aminu Muazu-Maifata ne ya bayyana hakan a yau Litinin, yayin da yake zantawa da manema labarai a garin Lafia na jihar Nasarawa.
Muazu-Maifata ya ce, daukacin Kananan Hukumomin kasar nan, suna samun sama da kashi 18 na kudaden da ake rabawa duk wata daga asusun tarayya.
Tun a baya ne dai Gwamnatin tarayya ta kayyade Naira dubu 62 a matsayin iya sabon albashin, wanda kungiyar kwadago ta bukaci gwamnati da ta biya Naira 494.