fidelitybank

Ba za mu gajiya ba har sai mun murƙushe Lakurawa a Kebbi – Ƴansanda

Date:

Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi, ta sha alwashin kawo karshen ‘yan fashi da miyagun laifuka a fadin jihar.

Hakan ya biyo bayan wani kazamin harin da wasu da ake zargin ‘yan kungiyar nan ne da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar ta Lakurawa ne suka kai a karamar hukumar Augie, inda mutane 16 suka mutu.

A cikin wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta fitar a ranar Litinin ta tabbatar da cewa ta tura tawagogin dabara domin farautar ‘yan ta’addan.

A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, CSP Nafiu Abubakar, harin ya afku ne a ranar Asabar, 6 ga watan Afrilu, 2025, da misalin karfe 6 na yamma, yayin da wasu mahara dauke da muggan makamai suka afkawa wasu kauyuka biyu.

“Maharani wadanda suka isa wurin da yawan gaske, sun yi awon gaba da wasu shanu da ba a tantance adadinsu ba, suka kuma yi artabu da jama’ar yankin, wanda ya yi sanadin asarar rayuka goma sha shida,” in ji sanarwar.

Da yake Allah wadai da lamarin, kwamishinan ‘yan sanda, Bello Sani, ya bayar da tabbacin cewa za a yi adalci cikin gaggawa.

Ya sanar da tura karin tawaga masu dabara da suka hada da ‘yan sanda, sojoji, jami’an tsaron Najeriya da jami’an tsaro na farin kaya, da ‘yan banga zuwa yankunan da rikicin ya shafa.

“Kudirinmu na kawar da ‘yan fashi da sauran miyagun laifuka a Jihar Kebbi ya tsaya tsayin daka, muna tura duk wani abu da ake da shi don ganin an gurfanar da wadanda suka aikata wannan aika-aika a gaban kuliya,” in ji CP Sani.

CSP Abubakar ya kara da cewa tun daga lokacin an dawo da zaman lafiya a yankunan da lamarin ya shafa, kuma ana ci gaba da gudanar da cikakken bincike.

Rundunar ‘yan sandan ta kuma yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu, su kuma ci gaba da bayar da hadin kai ga jami’an tsaro, tare da jaddada aniyar ta na kare rayuka da dukiyoyi a fadin jihar Kebbi.

naija news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp