Jam’iyyar APC a jihar Kaduna ta ce, ba ta da wani shiri na dakatar da tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai.
Rahotanni na cewa nan ba da jimawa ba za a dakatar da El-Rufai saboda ganawa da ya yi da wata jam’iyyar adawa a kwanakin baya.
Wani sako a daren Talata da Salisu Wusono, mai magana da yawun jam’iyyar APC a Kaduna, ya bayyana cewa ba wata magana ta dakatar da shi.
El-Rufai ya ziyarci shalkwatar jam’iyyar SDP da ke Abuja, kuma a kwanakin baya an gan shi tare da Abdul Ningi, Sanatan da a dakatar da shi a majalisa.
Sai dai ziyarce-ziyarcen dai ta jawo cece-kuce a shafukan sada zumunta, a daidai lokacin da ake ta yada jita-jitar cewa tsohon gwamnan Nasir El-Rufa’I na shirin wani yunkuri na barin APC.