Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani mahaluki a doron duniya, da zai ɗagawa kasarsa yatsa, ko yi mata barazana ko ci zarafinta.
Yana magana ne yayin da ya ke baje kolin manyan makaman da ƙasar ta mallaka, ciki har da makamai masu linzami na Nukiliya da ka iya kaiwa ko wanne lungu da saƙo na duniya.
An kuma nuna wasu manya manyan jiragen ruwan soji, da ka iya nutsewa a cikin ruwa harma su yi nisan akalla mita ashirin a karkashin ruwan.
A sararin samaniya, jiragen yaƙi masu layar zana sun yi ta shawagi, a wani salo na nuna wa duniya irin shirin da Chinar ta yi.
Ƙwararru a ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon da ma masana harkar tsaro a duniya na nan na ta nazartar faretin na China.