Hukumar zaɓe ta kasa INEC, ta ce dokokin Kundin Tsarin Mulkin ƙasar ba su ba ta damar ta ci gaba da yin aikin rajistar kaɗa ƙuri’a ba kafin babban zaɓe na 2023.
A ranar Talata ne rahotanni suka ambato Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta umarci hukumar ta ci gaba da aikin rajistar har zuwa saura kwana 90 kafin zaɓen.
Independent National Electoral Commission (INEC) ta rufe aikin rajistar zaɓen a watan Yuli da ya gabata, abin da ya jawo martani da koke-koke daga ƙungiyoyin farar hula cewa za a tauye wa miliyoyin ‘yan ƙasa haƙƙinsu.
Amma da yake magana ta cikin shirin Politics Today na kafar talabijin ta Channels TV a ranar Talata, Kwamashinan Wayar da Kan Masu Zaɓe na INEC Festus Okoye ya ce hukumar ba ta samu kwafin hukuncin ba tukunna.
Ya ƙara da cewa: “Abu ne da ba zai yiwu ba a tsarin Kundin Tsarin Mulki ga INEC ta ci gaba da aikin rajistar masu zaɓe.”
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, saura kwana 93 da awa 7 a fara kaɗa ƙuri’a a babban zaɓen da za a gudanar a watan Fabarairu, inda ‘yan Najeriya za su zaɓi shugaban ƙasa da gwamnoni da ‘yan majalisar tarayya da na jiha.