Jam’iyyar PDP, ta sha alwashin cewa, ba za ta ci gaba da yin tsokaci a kai-da-kai da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ke yi wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar.
Ku tuna cewa Gwamna Wike wanda ya bukaci shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu ya yi murabus a matsayin sharadin marawa Atiku baya a zaben da za a yi a watan Fabrairu, a lokuta da dama, ya tunkari tsohon mataimakin shugaban kasar.
A ranar Litinin, Wike, yayin da yake mayar da martani game da amincewa da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi da tsohon shugaban Atiku, Olusegun Obasanjo, ya yi, ya yi wa Atiku ba’a, yana mai cewa dole ne wani abu ya kasance ba daidai ba.
Da yake mayar da martani, PDP a wata sanarwa da kakakin kuma daraktan hulda da jama’a na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP, Sanata Dino Melaye, ya fitar dauke da sa hannun, ya bukaci Wike da ya ji kunya.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Ya kamata Wike ya ji kunya ganin yadda ya rika neman Atiku a kullum ta hanyar rashin mutuntawa da cin mutuncin mutumin da bai yi maka komai ba.
“Ina ba shi shawara da ya goyi bayan duk wanda yake so ya goyi bayan saboda ba za mu lamunta da son zuciya ba. Abin tambaya a nan shi ne, shin akwai wani abu da Wike bai damka wa Amaechi ba?
“Me yasa Prince Uche Secondus, Rt Hon. Austin Okpara, Sen. Lee Meaba, H:E Celestine Omehia, Chief Abiye Sikibo, Sen George Sekibo, Hon. Chinyere Igwe, da sauransu, sun bar shi da rashin sanin ya kamata ga Atiku. Tabbas wani abu ba daidai ba ne a wani wuri”.


