fidelitybank

Ba za mu biya dan ta’adda kudin fansa ba – Tinubu

Date:

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya umarci jami’an tsaro da kada su biya kuɗin fansar sakin kusan ɗalibai 300 da malaminsu da aka yi garkuwa da su makon da ya gabata daga wata makaranta da ke Kaduna a yankin arewa maso yammacin ƙasar.

Tinubu ya kuma umarci hukumomin tsaro da su tabbatar an kuɓutar da dukkan mutanen da aka sace ba tare da biyan ƴan bindigar kuɗin fansa ba, kamar yadda ministan yaɗa labarai, Muhammed Idris ya shaida wa ƴanjarida a ranar Laraba.

Ministan ya ce shugaba Tinubu ya faɗa wa sojojin da ke laluben inda ɗaliban suke su tabbatar “ba a biya ko sisin kwabo ba”.

Tun farko, ƴan’uwan ɗaliban da ke tsaren sun ce ƴanbindiga sun buƙaci a biya su kuɗi mai yawa domin su saki yaran da suka sace daga makarantarsu a ƙauyen Kuriga.

Cikin makon da ya gabata, an sace mutane da dama ciki har da fiye da mutum 60 daga wani ƙauye a dai jihar ta Kaduna.

Cikin shekara uku da ta gabata, ɗaruruwan ɗalibai aka sace. Wasu a cikinsu an sake su bayan tattaunawa da hukumomi duk da cewa jami’ai sun musanta biyan kuɗin fansa.

Wata doka da aka amince da ita a 2022 ta hana biyan kuɗin fansa ga masu garkuwa.

Ƙaruwar sace-sacen mutane na zama ƙalubale ga gwamnatin Tinubu da ta yi alƙawarin magance matsalar tsaro.

nhgsfp

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp