Kulngiyar Napoli ta ce ba za ta amince da duk wani tayin da Manchester United za ta yi wa dan wasanta na Najeriya Victor Osimhen ba, idan aka sake bude kasuwar musayar ‘yan wasa a watan Janairu.
United ta raba gari da kyaftin din Portugal, Cristiano Ronaldo a wannan makon kuma rahotanni sun bayyana Osimhen a matsayin wanda zai maye gurbinsa.
Napoli na neman lashe kofin gasar farko cikin shekaru sama da ashirin kuma suna ganin Osimhen a matsayin babban dan wasa wajen cimma wannan burin.
Dan wasan mai shekaru 23 ya zura kwallaye tara a wasanni 11 da ya buga wa Partenopei a kakar wasa ta bana.
Napoli ba ta ci nasara ba a gasar Seria A bana, kuma ta samu tazarar maki takwas tsakaninta da AC Milan ta biyu.
“Victor Osimhen ba zai kasance a watan Janairu ba saboda Napoli na son ci gaba da kasancewa tare da shi a matsayin tauraruwarsu a kalla har zuwa karshen kakar wasa,” in ji Fabrizio Romano, masanin kasuwar canja wuri, ya shaida wa Givemesport.
“Haka kuma, wasu ‘yan wasa da yawa da ake yayatawa ba za su samu ba, don haka zai yi wahala a sami dan wasan da ya dace.”
Chelsea da Liverpool da Real Madrid kuma sun yi rade-radin suna zawarcin dan wasan.