Amurka ta ƙi amincewa da bukatar Rasha ta musayar manyan fursunoni tsakaninsu.
Ma’aikatar tsaron Amurka ta zargi Moscow da gaza mayar da hankali domin cimma matsaya kan batun duk da tsokacin da ta yi a jiya Juma’a.
Sai dai Mukaddashin Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergei Ryabkov ya ce cikin waɗanda ake fatan yin musayar har da wani fitaccen dilan makamai dan kasar Viktor Bout.
Rahotannin da ke fitowa daga Washington sun ce wata da watanni Amurka ta yi tana shirin musayar Mr Bout da wasu Amurkawa biyu da ake tsare da su a Rasha.
Ɗaya daga ciki ‘yar wasan kwallon kwando ce mai suna Brittney Griner, da tsohon ma’aikacin hukumar shige da fice Paul Whelan.