Kwamitin majalisar wakilai mai kula da albarkatun man fetur, ya bukaci gwamnatin tarayya da kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) da su yi biyayya ga tsohon farashin mai.
Shugaban kwamitin Alhassan Ado-Doguwa a wata sanarwa da ya fitar a Abuja, ya bayyana karin farashin man fetur a matsayin abin da ba za a amince da shi ba.
Ya ce, yanayin da kamfanoni masu zaman kansu suka yi amfani da gibin da ke tattare da tsarin wajen samun riba ba bisa ka’ida ba tare da kashe ‘yan Najeriya yana da illa ga ci gaban kasar.
“Muna kira ga Gwamnatin Tarayya da kuma, ba shakka, NNPCL da su yi la’akari da halin da ‘yan Najeriya ke ciki tare da dakatar da wannan karin farashin famfo na kwanan nan,” in ji shi.
A cewarsa, a halin yanzu ’yan Najeriya na fuskantar kalubale da dama.
“Bari mu koma kan tsohon farashin famfo da wuri-wuri kuma mai yiwuwa mu kara himma tare da manyan masu ruwa da tsaki don magance matsalar,” in ji shi.