Ƙoƙarin Najeriya na zama dunƙulalliyar ƙasa, ya gamu da gagarumin koma-baya, tun daga shekara ta 2015.
Tsohon Shugaban ƙasar, Cif Olusegun Obasanjo ne ya bayyana hakan, ta cikin ƙarshen mako a wani ɓangare na bikin cika shekara 85 da haihuwa lokacin wani taron ƙasashen duniya a Cibiyar tabbatar Tsaron Bil’adama da Tattaunawa da ke Ɗakin Karatun Shugaba Olusegun Obasanjo a Abeokuta cikin jihar Ogun.
Sai dai a na ta martanin fadar gwamnatin Najeriya ta ce, ba za ta yi sa-in-sa da mai shekarun tsufa kamar Obasanjo ba. In ji BBC.