William Ruto, wanda aka ayyana a matsayin wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasa a Kenya makon daya gabata, ya yi na magana a karon farko tun bayan da abokin takararsa Raila Odinga, ya yi watsi da sakamakon zaben, in da yace zai bayar da dama ga mutane su fadi ‘yanci albarkaci bakinsu da kuma tabbatar da dimokradiyya ta gaskiya.
Mr Ruto, ya ce zai kawo karshen duk wata barazana da tsoratarwa a kasar.
Ya ce, ” Ina son yi wa al’ummar Kenya alkawarin cewa gwamnatinmu ba ta da hannu ko alaka da irin barazanar da ake gani a yanzu.”
Ya ci gaba da cewa,” Zamu dawo da dimokradiyyarmu ta da.” In ji BBC.


