Fadar shugaban ƙasa ta ƙaryata zargin da ake na rashin jituwar da ke tsakanin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima, inda ta bayyana cewa dangantakar shugabannin biyu na nan da ƙarfinta.
Babban mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa ga mataimakin shugaban ƙasa, Stanley Nkwocha ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwar da ya fitar a bikin cika shekaru 58 na mataimakin shugaban ƙasar, Kashim Shettima.
Nkwocha ya bayyana zargin a matsayin “makirci mara tushe waɗanda ba su nuna gaskiyar lamari a Aso Rock”.
Sanarwar ta jaddada cewa Shettima wani muhimmin ɓangare ne na gwamnatin Tinubu inda yake bai wa Tinubu cikakken goyon baya da kuma ƙwarin gwiwa.
Talla
Da yake watsi da jita-jitar rashin jituwa tsakanin Tinubu da Shettima, Nkwocha ya sake nanata biyayyar Shettima ga gwamnatin Tinubu.
Ya bayyana kwazon Shettima da jajircewarsa ga shugaba Tinubu, inda ya bayyana cewa biyayyar mataimakin shugaban ƙasa da hadin gwiwarsu sun taimaka wajen samun kyakkyawan yanayi da hadin kai a cikin gwamnatin.
Da yake magana kan rahotannin cewa Shettima yana jinya, Nkwocha ya ce waɗannan ikirari ba su da tushe.
A ƙarshe ya jaddada irin gudummawar da Shettima ke bai wa gwamnatin Tinubu, inda ya nuna cewa mataimakin Shugaban kasa ya kawo wani nau’i na kwarewa da kuzari na musamman don tallafa wa manufofin Tinubu ga Najeriya.