Dan takarar shugaban kasa na jamâiyyar African Action Congress, AAC, a zaben 2023, Omoyole Sowore, ya ce babu wata maboya da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai samu bayan ya sauka.
Sowore ya ce dole ne Buhari ya girbi abun da ya shuka na cin zarafin dan Adam.
Ya na mai da martani ne kan kalaman Buhari na komawa Jamhuriyar Nijar bayan 29 ga Mayu.
Buhari ya sha alwashin komawa Jamhuriyar Nijar daga garin Daura na jihar Katsina idan har zaman lafiyarsa ya tabarbare.
Ya yi wannan jawabi ne a gidan gwamnatin jihar yayin da ya karbi bakuncin wasu mazauna babban birnin tarayya karkashin jagorancin minista Muhammad Musa Bello a wajen bikin sallar Eid-el-Fitr.
âBa zan iya jira in koma gida Daura ba. Idan sun yi wata hayaniya ta dame ni a Daura, zan tafi Jamhuriyar Nijar. Da gangan na shirya don yin nisa sosai.
“Na sami abin da nake so kuma zan yi ritaya a nitse zuwa garinmu. Duk da fasahar zamani ba zai yi sauki ba zuwa Daura,â inji shi.
Da yake mayar da martani, Sowore ya ce komai dadewa za a sa Buhari ya biya kudin taâasar da ya yi.
Sowore ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa: âShugaba @Mbuhari, ka yi hakuri, ba za a buya ga miyagu ba. Dole ne ku biya bashin da kuka aikata na cin zarafin bil’adama.
âHar Ĉarshen zamani, zaluntar ku za ta cinye ku. Komai tsawon lokacin da zai Éauka, ba zai damu da inda kuka Éoye ba, zaku amsa laifinku. #Revolution yanzu.”


