fidelitybank

Ba wata jam’iyyar da na ke goyon baya – Kwankwaso

Date:

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, Sen. Rabi’u Musa Kwankwaso ya karyata rade-radin da ake yadawa cewa yana yiwa wata jam’iyya aiki a zaben 2023 mai zuwa.

Kwankwasko ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyi daga wasu magoya bayansa a lokacin da yake gabatar da shirin rediyo kai tsaye a birnin Dutse na jihar Jigawa.

Ya ce, tun lokacin da shi da magoya bayansa suka koma jam’iyyar NNPP, wasu mutane ke hada karairayi iri-iri saboda dalilansu na siyasa.

A cewarsa, “Na ji wasu na cewa dattawan Arewa sun gana da ni, sun ce in bar dan takarar Arewa, wasu kuma na cewa ina soyayya da APC.

“Wa zai iya gaya mana Arewa? Wa ya fi mu sanin Arewa? Waɗannan ‘yan takara ne waɗanda ke da matsala game da cancantar su da lafiyarsu. ”

Ya bayyana cewa wannan labarin ba shi da tushe balle makama kuma wasu bata gari ne suka shirya shi saboda wasu dalilai na siyasa domin su dauke hankalin ‘yan Najeriya.

“Allah ya kiyaye na yi aiki ko soyayya da APC, PDP, ina jam’iyyar NNPP ne, babu gudu babu ja da baya.

“Wannan wata dama ce ta zinari ga dukkan ‘yan Najeriya idan suna son abubuwa su canja da kyau. NNPP ita ce amsar kuma idan suna son abubuwa su ci gaba da kasancewa,” ya kara da cewa.

latest news nnn

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An kashe kwamandan Boko Haram a tafkin Chadi

Sojojin Jamhuriyar Nijar sun sanar da kisan wani jagoran...

Hisbah za ta yi wa ‘yan Daban Kano aure

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta sanar da wani...

Ganduje ya dawo Najeriya bayan ya shafe wata guda a Landan

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Ganduje,...

Barrister Sa’idu ya kama aiki bayan ya maye gurbin Muhyi Magaji

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya rantsar...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

Barau zai mayar da filin wasan BUK na zamani

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya...

Jami’ar Bayero ta Kano ta yi sabon shugaba

Farfesa Haruna Musa, ya karɓi ragamar shugabancin jami’ar Bayero...

Gwamnatin Kano ta amince Barau FC ta yi wasa a filin Sani Abacha

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kungiyar kwallon kafa...

Gwamnatin Tinubu na takalar Kwankwaso da fada – Buba Galadima

Jigo a jam'iyyar NNPP, kuma na hannun tsohon gwamnan...

Newcastle United ta dauki dan wasan tsakiya Jacob daga Aston Villa

Newcastle United ta sanar da daukar dan wasan tsakiya...
X whatsapp