Rundunar ‘yan sandan birnin tarayya Abuja, ta yi watsi da rahotannin da ke cewa an kashe mutane kusan 30 a karamar hukumar Kuje.
Rahotannin da ba a tabbatar da su ba sun fito a makon da ya gabata na cewa mutane 30 ne suka mutu sakamakon zaftarewar kasa a babban birnin kasar sakamakon ayyukan masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba.
Rahotonni ya fito ne daga taron farko da ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike da shugabannin kananan hukumomi shida suka yi a ranar Alhamis din da ta gabata.
Sai dai kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Haruna G. Garba, a wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Josephine Adeh ya fitar ranar Talata, ya karyata rahoton a matsayin karya.


