Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC, ta karyata rahotannin da ke nuni da cewa za a fara yajin aikin a fadin kasar nan a ranar Litinin 18 ga watan Disamba.
Wata sanarwa da shugaban yada labarai da hulda da jama’a na NLC, Beson Upah ya fitar a ranar Lahadi, ta ce sanarwar da ake yadawa a shafukan sada zumunta na bogi ne.
Ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi watsi da sanarwar, yana mai jaddada cewa babu wani shiri na shiga yajin aikin.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “An kawo mana sanarwar shiga yajin aikin (wadda aka ce babban sakataren NLC da Sakatare Janar na TUC, Comrades Emmanuel Ugboaja da Nuhu Toro suka sanya wa hannu) zai fara aiki gobe Litinin 18 ga watan Disamba. a fadin kasar.
“Muna so mu sake tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa wannan sanarwar ba ta fito daga gare mu ba, kuma ba mu da niyyar fara wani yajin aiki a wannan lokacin.
“Saboda haka, an shawarci ‘yan Najeriya da suka damu da su yi watsi da wannan sanarwar. karya ne”.