fidelitybank

Ba wani wulakanci ko abun kunya game da komawar Rashford Aston Villa – Amorim

Date:

Kocin Manchester United Ruben Amorim ya ce, babu wani abin kunya ko wulakanci game da batun aro na Marcus Rashford zuwa Aston Villa.

Ya ce irin wannan yunkuri na iya taimakawa ‘yan wasa su inganta kansu.

Rashford ya amince ya koma kungiyar ta Premier League Aston Villa aro na tsawon watanni shida bayan da kocin ya bayyana cewa baya cikin shirinsa.

Kungiyar Unai Emery za ta biya akalla kashi 75% na albashin Rashford fam 365,000 a mako kuma suna da zabin siyan shi kan fan miliyan 40 a bazara.

Da yake magana bayan Crystal Palace ta lallasa Red Devils da ci 2-0, an tambayi Amorim ko aika dan Ingila a matsayin aro zuwa kungiyar da ke saman tebur abin kunya ne.

“Ba abin kunya ba ne. Lokacin da kake ba da aron dan wasa-kuma ban sani ba, ina tsammanin ba a hukumance ba-lokacin da ka ba dan wasa aro, kana tsammanin zai taka leda kuma ya inganta, don haka babu wani abin wulakanci a can.

“Na fahimci tambayar, amma kawai na mai da hankali kan ‘yan wasa na, shi ke nan. Don haka idan taga ya rufe, hakika zan mai da hankali sosai kan kungiyarmu kawai da inganta kungiyarmu.”

Ya kuma yi magana game da tafiyar Rashford da ke tasiri kasuwancin hunturu, ya kara da cewa: “Za mu gani. Akwai ƙarin kwana ɗaya; mu jira sai taga ya rufe”.

nigeria 
news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp