Tsohon Ministan Sufuri a Najeriya Rotimi Amaechi ya ce an daina jin ɗuriyarsa ne a fagen siyasar Najeriya saboda “babu wani sabon abu” da zai faɗa.
Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya riƙe muƙamin minista a gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari daga 2015 zuwa 2022, bayan ya mulki jihar tasa a kudancin Najeriya tsawon shekara takwas.
“Babu wani sabon abu kwatakwata,” in ji ɗan siyasar wanda ya nemi takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC mai mulki cikin hira ta musamman da BBC.
“Abubuwan da ake so na yi magana a kan su suna nan kuma tun shekarun 1970 aka fara magana a kansu. Talauci, yunwa, rashin ingataccen ilimi, fashi, sata, cinhanci da rashawa, duka suna nan. Akwai abin da ya sauya ne?”


