Gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya musanta jita-jitar da wasu ke yi cewa, yana sha’awar kujerar shugaban ma’aikata a sabuwar gwamnatin zababben shugaban Bola Ahmed Tinubu da za a kafa karshen watan Mayun shekarar na ta 2023.
Gwamna El-Rufai ya musanta rade-raden ne ranar Asabar a jihar Gombe yayin tattaunawa da manema labarai.
Gwamnan ya je jihar ta Gombe ne domin kaddamar da aikin gina gidaje 550 da gwamnan jihar Muhammad Inuwa Yahaya zai yi.
El-Rufai ya ce hasashen da mutane ke yi maganganu ne kawai na kan titi.
Ya kara da cewa ba dole ne sai mutum ya kasance cikin gwamnati ba kafin ya taimaka wajen ci gaban Najeriya, don haka ko baya cikin gwamnati zai dukufa wajen ciyar da ita gaba a cewarsa.
“Ban tattauna da zababben shugaban kasa kan wannan batun ba don haka ba na son jita-jita.
“Na karanta yadda ake ta danganta ni da mukamai daban-daban a wasu jaridu, to amma kun san ni dan Najeriya ne da ya dukufa wajen ciyar da ita gaba” in ji El-Rufai.