fidelitybank

Ba wani jami’i ko Minista da zai kara fita kasar waje – Tinubu

Date:

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya haramta tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje na tsawon wata uku ga ministoci da shugabannin ma’aikatu da hukumomin gwamnati.

Shugaban ma’aikata a fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila ne ya sanar da umarnin cikin wata takarda da aka aikewa sakataren gwamnatin tarayya, George Akume.

An bayyana ƙalubalen tattalin arzikin da ake fama da shi da buƙatar alkinta kuɗin gwamnati da ake kashewa yayin irin waɗan nan tafiye-tafiye a matsayin dalilan da suka sa aka ƙaƙaba haramcin kan tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje.

Takardar ta ce jami’i na buƙatar amincewar shugaban ƙasa idan yana son a ɗage masa haramcin kuma dole a yi hakan mako biyu kafin lokacin tafiyar.

Matakin na zuwa ne bayan bulaguron baya-bayan nan da ofishin akanta janar na ƙasa ya yi da ta janyo cece-kuce.

Ofishin ya gudanar da wani taron ƙarawa juna sani a birnin Landan wanda ya samu halartar kwamishinonin kuɗi da jami’ai daga ofishin akanta janar.

A baya dai al’umma sun yi ta tsokaci a kai, abin da suka ce ya zo ne a lokacin da ƙasar ke fuskantar ƙalubalen tattalin arziki da kuma tashin dala da ke shafar darajar kuɗin naira.

hausa news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp