A lokacin zaɓen shugaban ƙasa an samu mutane da dama waɗanda suka fito, domin kaɗa ƙuri’a a Port Harcourt na jihar Rivers.
A zaɓen na shugaban ƙasa wanda ya gudana a ranar 25 ga watan Fabarairu, mutane sun isa rumfuna suka jira isowar jami’an zaɓe, sai dai wannan karo ba haka abin yake ba.
Madam Victoria Briggs ta ce, ba ta ji daɗin yadda aka yi zaɓen shugaban ƙasa ba, shi ya sa ba za ta yi zaɓen gwamna ba.
Karanta Wannan: Kowa ya zabi ra’ayin sa – Buhari
“Ba na murna, wancan zaɓen da muka yi an watsar da ƙuri’unmu, saboda haka mene amfanin na sake fitowa kaɗa ƙuri’a?”
A rumfar zaɓe ta 04, yanki na 02 aikin zaɓe na ci gaba da gudana, amma babu mutane da yawa.
A lokacin zaɓen shugaban ƙasa an samun jinkirin isowar masu aikin zaɓe a wannan mazaɓa, amma a wannan karo komai ya iso kan lokaci.
Sai dai kuma masu kaɗa ƙuri’a sun ƙi fitowa.