Hamas ta ce ba za ta ƙara sakin ƴan Isra’ila da take garkuwa da su ba har sai an tsayar da yaƙi.
Hamas ɗin ta ce ƙungiyoyin Falasɗinawa sun dakatar da shirin sakin ƙarin mutane har sai Isra’ila ta amince ta kawo karshen yaƙi a Gaza.
A wani sako cikin harshen Larabci da Hamas ta fitar a shafin Telegram, ta ce: “Akwai matakin da Falasɗinawa suka ɗauka na ƙasa baki-ɗaya cewar babu wata tattaunawa kan musayar fursunoni da waɗanda ake garkuwa da su har sai bayan Isra’ila ta amince ta kawo karshen yaƙi.”
Ba a dai san wasu ɓangarori ne na Falasɗinawa be ke da alaka da wannan sanarwa.
Islamic Jihad, wata karamar ƙungiya a Zirin Gaza, ita ma tana rike da wasu ƴan Isra’ila.
Ana ci gaba da tattaunawa don cimma sabon yarjejeniya kan yaƙin a Alkahira, babban birnin Masar, duk da cewa tattaunawa da aka yi da farko ba ta cimma komai ba, inda aka ruwaito Hamas na cewa ba za su amince da wata yarjejeniyar tsagaita wuta na wucin-gadi ba.
Lokacin da aka tsagaita wuta na kwanaki shida a watan Nuwamba, an saki ƴan Isra’ila 105 da ake garkuwa da su bayan musaya da Falasɗinawa da ake tsare da su a gidajen yarin Isra’ila.
An yi imanin cewa har yanzu akwai ƴan Isra’ila 120 da ake rike da su a Gaza.
Isra’ila ta sha kin amincewa da yarjejeniyar tsagaita na dindindin da Hamas, inda ministan tsaron Isra’ila Itamar Ben Gvir, ya ce tsagaita wuta kafin karya lagon Hamas da kuma mayar da dukkan waɗanda ake garkuwa da su da cewa zai zama gazawa.


