Tsagin jam’iyyar NNPP ta Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya sanar da korar ‘yan kwamitin amintattun da suka dakatar da jagoran nasu na kasa, Kwankwaso.
Ɗaya daga cikin jigo a jam’iyyar da ke biyayya ga Kwankwaso, Injiniya Buba Galadima ya shaida wa BBC cewa sun ɗauki wannan mataki ne a wani taro da suka gudanar a Abuja a wani yunkurin na fasalta al’amuran jam’iyyar.
Wannan mataki na zuwa ne bayan a jiya Talata wani ɓari na jam’iyyar ta NNPP ya bayar da sanarwar dakatar da Rabi’u Kwankwaso daga jam’iyyar bisa zargin yi wa jam’iyyar zangon-kasa


