Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce, sun bi duka ƙa’idojin da suka dace wajen soke dokar masarautun jihar.
Yayin da yake gabatar da jawabi a gidan gwamnati lokacin miƙa takardar kama aiki ga sabon sarki, Gwamna Abba Kabir ya ce inda akan bin ƙa’ida ne to ba sa jin tsoron kowa.
A jiya ne dai wata kotun tarayya ta bayar da umarnin dakatar da soke masarautun, bayan da Alhaji AMinu Babba Dan Agundi ya shigar da ƙara a gabanta, yana neman a soke sabuwar dokar.
To sai dai cikin martanin da ya mayar game da hukuncin kotun, Abba Gida-gida ya ce dama tun da farko abin da ya hana su rushe masarautun da wuri shi ne nazari da kuma tuntubar ƙwararru don tabbatar da bin ƙa’ida.
”Kuma haka siddan ba za mu lamunci wani alkali yana can wata ƙasar ya bayar da umarnin a kan abin da muka bi ƙa’ida ba”, in Abba Kabir Yusuf.
Sarki Muhammadu Sanusi II zai jagoranci sallar Juma’a a masallacin gidan gwamnatin jihar, ba kamar yadda aka tsara a baya cewa a masallacin kofar kudu ba