Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Riba ya c,e gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansa ba wai yakar kowa ba.
Fubara ya bayyana haka ne a yayin kaddamar da rukunin gidaje 20,000 na masu karamin karfi a jihar a Mbodo-Aluu, daura da titin filin jirgin sama na kasa da kasa a karamar hukumar Ikwerre a ranar Juma’a.
Ya sha alwashin ci gaba da yin abin da ya dace a gaban Allah da kuma mutane tare da karfafa gwiwar jama’a da su shiga harkokin mulki.
A cewar Fubara: “Ga mutanenmu, ina so in tabbatar muku, gwamnatinmu ba ta da wata alaka da fada da kowa.
“Gwamnatinmu ita ce kulawa da kare mutanenmu. Ina mai tabbatar muku da cewa wannan shi ne farkon hidimar da muke yi wa al’ummar Jihar Ribas.
“Ba hidima ga manyan mutane ba ne amma ga talakawa da masu karamin karfi. Wadannan su ne mutanen da muke son tsayawa tare kuma muna tare da su daga yau.”
Wannan yana zuwa ne a cikin ci gaba da rashin jituwa tsakanin Wike da Fubara.