Majalisar tsaron Iran ta cire sunan tsohon shugaban ƙasar, Mahmoud Ahmadi Najad daga jerin sunayen ‘yan takarar shugabancin ƙasar a zaɓen da za a yi a ƙarshen watan da muke ciki.
Tuni dai majalisar ta amince da sunayen mutum shida ciki har da mataimakin shugaban ƙasar, Mohammad Mokhber da Amir-Hossein Ghazizadeh Hashemi da kakakin majalisar dokokin ƙasar, Mahmoud Bagher Ghalibaf
Haka ma majalisar ta cire sunan tsohon kakakin majalisar dokokin ƙasar, Ali Larijani.
An dai ɗage zaɓen ƙasar ne bayan rasuwar tsohon shugaban ƙasar, Ebrahim Raisi da ya mutu a hatsarin jirgin sama a watan da ya gabata.