fidelitybank

Ba shugaban da zai iya kawo karshen ta’addanci a Najeriya – Lai

Date:

Ministan yada labarai da raya al’adu, Lai Mohammed, ya ce babu wani shugaba da zai ce shi ne zai iya kawo karshen ayyukan ’yan ta’adda a shekara mai zuwa.

Ministan ya yi wannan kakkausar martanin ne bayan an tambaye shi a wani taron manema labarai, cewa ko kalubalen tsaron da a ke fuskanta a halin yanzu zai kawo karshe kafin shugaba Buhari ya sauka daga mukamin sa a shekarar 2023. A cewar Aminiya.

Lai Mohammed sai ya ce,”Ba na tsammani ko shugaba Buhari ba shi da tabbacin cewar za a iya murkushe ayyukan ’yan bindiga a shekara mai zuwa, kuma zargin da a ke yi wa shugaba Buhari na rashin katabus wajen kare rayukan al’umma da a ke kashewa kusan a kullum”.

A makon nan ne dai, tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa, Buhari ya yi iya kokarinsa, babu wani abin da zai iya tabukawa fiye da hakan a nan gaba.

Matsalar tsaro dai a Najeriya ta yi kamari sosai, musamman a yankin Arewacin Najeriya, inda ta sa mutane da dama fusata har a ka shiga yi wa Buhari zanga-zanga, domin kawo karshen zubar da jinin al’umma da a ke yi a yankin.

legit.news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Yunwa na kara tsananta a arewa maso gabashin Najeriya – ICRC

Kungiyar agaji ta Red cross (ICRC) ta bayyana yadda...

Ba zan taba watsawa Tinubu kasa a ido ba – IBB

Ɗan tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, wato...

Natasha kar ki kuskura ki dawo aiki – Majalisa

Majalisar Dattijai ta buƙaci Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta dakatar...

Za a yi ruwan sama da iska mai ƙarfi a jihohi harda Kano – NiMET

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMET) ta fitar...

Obi da El-Rufa’i za su koma jam’iyyar mu a hukumance – ADC

Sakataren yada labarai na rikon kwarya na jam’iyyar African...

Za mu tattauna da tarayyar Turai a kan Nukiliyarmu – Iran

Iran ta tabbatar cewa za ta gudanar da tattaunawa...

Mu na gargadin Isra’ila kan korar al’ummar Gaza daga yankin su – MDD

Hukumar kula da ayyukan jin-ƙai ta Majalisar Ɗinkin Duniya...

Rikici ya kuma balle a Syria

Ƙungiyoyin kare haƙƙin dan'adam sun ce, wani sabon rikici...

Tsofaffin ‘Yansanda na da ‘yancin yin zanga-zanga – A Cewar Amnesty

Ƙungiyar Amnesty International ta ce tsofaffin ƴansandan Najeriya girmamawa...

Buhari ya yi wa Najeriya hidimar da ba za a manta da shi ba – António Guterres

Babban Sakatare na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) António Guterres...

Binani ta koma jam’iyyar haɗaka ta ADC

'Yartakarar gwamnan jihar Adamawa a zaɓen 2023, Sanata Aishatu...

A Talata zan koma aiki na a majalisa – Natasha

Yar majalisar Dattawa, Sanata Natasha Akpoti, ta ci alwashin...
X whatsapp