Shugaba Lula Inacio da Silva na Brazil ya kori Shugaban rundunar sojin ƙasar, makonni biyu bayan kutsen magoya bayan Jair Bolsonaro da ya gada.
A cewar ministan tsaro Jose Mucio, lamarin ya haifar da rashin amincewa da juna tsakanin rundunar soji da gwamnati, kuma abu ne da dole a ɗaukar masa mataki.
Yanzu haka ana tsare da gwamman sojoji da ‘yan sanda da ake zargi da haɗa baki da masu boren a lokacin.
Za a maye gurbin Janar Julio Cesar de Arruda da Janar Tomas Ribeiro Paiva, wanda na hannun damar Shugaba Lula da Silva ne.