fidelitybank

Ba sa hannun Buhari wajen cire dala miliyan 6.2 da CBN ta yi

Date:

An ci gaba da shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele a babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda aka tabbatar wa kotu cewa binciken kimiyya ya nuna cewa an yi amfani da sa hannun bogi na tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari wajen cire kuɗi dala miliyan 6.2 don daukar nauyin masu sanya idanu na ƙetare a zaɓukan ƙasar.

Wani shaida da EFCC ta kira, mai suna Bamaiyi Meriga ya tabbatar wa kotu ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Hamza Muazu cewa, binciken kimiyya da aka yi wa takardun da aka sanya hannu a kansu domin cire kudin, ya nuna cewa sa hannu da hatimi da aka yi amfani da su wajen cire kudin ba daidai suke da na ainihi ba.

Ya kuma tabbatar da cewa sa hannun ba na tsohon shugaban najeriya Muhammadu Buhari ba ne, kuma ba na tsohon sakataren gamnatin tarayya, Boss Mustapha ba ne.

An gabatar wa alƙalin da ke jagorantar shari’ar takardun biyu, masu ɗauke da umarnin shugaban ƙasa a matsayin shaida, sannan kuma ya amince da su.

Bayan da lauyoyin Emefiele suka nuna ƙorafinsu game da takardun, shaidar ya ce shi ba ma’aikacin EFCC ba ne kuma ba hukumar ce ke biyan sa ba.

Lauyan Emefiele, Matthew Burkaa, ya nuna rashin amincewarsa da shaidar, yana mai cewa shaidar ya yaudari kotun ne don kauce wa tambayoyin da za a yi masa.

To sai dai lauyan masu shigar da ƙara, Rotimi Oyedepo, bai ji dadin kalaman lauyan wanda ake ƙarar ba.

An dai ɗage shari’ar zuwa ranar 1 ga watan Maris domin ci gaba da shari’ar.

Emefiele na fuskantar shari’a a kotun kan laifuka 20 da suka ƙunshi zargin cin hanci da haɗin baki da cin amana da amfani da sa hannun bogi wajen cire kudi har dala 6,230,000.

Ana zargin sa da sa hannun bogi na tsohon sakataren gwamnatin ƙasar Boss Mustapha wajen ciye kuɗin ta hanyar da ba ta dace ba.

mmm.nnn.

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp