Gwamnan jihar Jigawa, Muhammadu Badaru Abubakar, ya ce, babu gaskiya a zargin da ake musu ne cewa, wasu daga cikin gwamnonin Arewa sun yi kane-kane sun hana ruwa gudu a jam’iyyar ta APC.
A tattaunawa da Editan BBC, gwamnan ya soma ne da bugun kirji cewa, jam’iyyar APC ta taka rawar gani tsawon lokacin da ta shafe a kan mulkin.
Rikicin da ya dabaibaye APC na zuwa ne a yayin da jam’iyyar APC mai mulkin kasar ke shirin gudanar da babban taronta a karshen wannan watan, wani jigo a jam’iyyar ya ce, ba suda wani zabi illa bin dan takarar da shugaba Muhammadu Buhari ya ke goyon baya.