fidelitybank

Ba ruwan Biri da gada a makamin Nukiliya – Shettima

Date:

Mataimakin shugaba Najeriya Kashim Shettima ya ce ƙasar za ta ci gaba da aiki da haramcin gwajin makaman nukiliya.

Shettima ya bayyana hakan ne a lokacin ganawa da tawagar hukumar yarjejeniyar hana gwajin makaman nukiliya ƙarƙashin jagorancin sakataren zartarwarta, Dr Robert Floyd, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Mataimakin shugaban ƙasar ya ce Najeriya kamar sauran ƙasashen Afirka da dama na fama da tarin matsaloli na zamantakewa da tattalin arziƙi da suka haɗa da fatara da talauci da sauyin yanayi.

Ya ce yanzu babban abin da ke gaban Afirka shi ne ta ga ta shawo kan matsalolin da ke barazana ga wanzuwarta – na fatara da kuma tasirin sauyin yanayi, amma ba batun mallakar makaman nukiliya ba.

A nasa ɓangaren jagoran tawagar hukumar, Dr Robert Floyd, ya yaba da ƙoƙarin Najeriya wajen cimma muradun hukumarsa.

Sannan kuma ya yaba da shugabancin Najeriya ƙarƙashin Bola Tinubu wajen bayar da gudummawar rage gwaje-gwajen makaman nukiliya a duniya, kamar yadda ya ce.

bbc nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

JAMB ta amince da maki 150 mafi ƙanƙanta don samun gurbin karatu a jami’o’i

Hukumar shirya jarrabawar shiga Jami'o'i ta Najeriya (JAMB) ta...

ASUU ta dakatar da yajin aikin da ta fara

Ƙungiyar Malaman Jami'o'i ta Najeriya, ASUU da dakatar yajin...

Masu haɗakar ADC na ɓaɓatu ne saboda rashin gwamnati – Radda

Gwamnan jihar Katsina, Mallam Dikko Umar Radda ya yi...

Ba ruwan Biri da gada a makamin Nukiliya – Shettima

Mataimakin shugaba Najeriya Kashim Shettima ya ce ƙasar za...

An kashe Mutane 70 a jihar Filato

Rahotonni daga jihar Filato na cewa ƴanbindiga sun kai...

Ambaliya ta kashe mutane 100 a Amurka

Hukumomi a jihar Tesxas da ke Amurka sun bayyana...

Tsohon Ministan kuma jigo a PDP ya koma ADC

Tsohon ministan harkokin ‘yan sanda kuma sau uku a...

Trump ya caccaki Elon Musk

Shugaban Amurka Donald Trump ya caccaki tsohon mashawarcinsa, Elon...

Dalilin da ya sa Kwankwaso ya ki shiga jam’iyyar hadaka – Galadima

Jam'iyyar NNPP ta ce abin da ya sa ba...

Obi ba zai taba zama shugaban kasa ba – Wike

Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce, tsohon ɗan takarar...

Ƴansanda sun kama ƴan Ghana 19 da aka yi safararsu a Najeriya

Rundunar ƴansandan Najeriya ta kuɓutar da wasu ƴan Ghana...

Benue da Edo da Bayelsa na fargabar balewar madatsar ruwan Kamaru

Gwamnatocin jihohi uku na cikin shirin ko-ta -kwana, sakamakon...
X whatsapp