Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya musanta nuna goyon bayan ɗan siyasar Najeriya kuma dan takarar shugaban ƙasa Peter Obi, biyo bayan yaɗa jita-jitar faruwar haka akan shafukan zumunta na kasashen biyu da ke yammacin Afirka.
Shugaba Akufo-Addo ya ce wannan batu “karya ce kuma neman rigima ne”.
“Ghana da Najeriya sun shafe gomman shekaru da kyakkyawar dangantakar mai karfi tsakanins su, sun zama kamar ƴan uwa.
“Kuma ba zan zama wanda zai tsoma baki a kan lamuran cikin gida na siyasar Najeriya ba,” ya ce a shafin Twitter.
Peter Obi na takarar shugabancin kasa a ƙarƙashin jam’iyyar ƙwadago ta Labour.
Najeriya za ta zabi sabon shugaban a watan Fabrairun 2023.