Gabanin zaben 2023, Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo, a ranar Talata, ya bayyana cewa, baya son hada kai da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, yana mai jaddada cewa, kasuwancin sa shine tallata dan takarar shugaban kasa Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu, a yankin Kudu maso Gabas.
Uzodinma ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels.
Ya yi nuni da cewa akwai ‘ya’yan jam’iyyar APC da dama a yankin Kudu maso Gabas masu ‘biyayya’ ga jam’iyyar.
Uzodinma ya ce, “Ni dan siyasa ne kuma jam’iyya ta APC ce kuma ina da dan takara na a jam’iyyar. Kuma na san muna tuntuba da magana da jama’armu domin su zabi dan takararmu.
“Na damu da yi wa jam’iyyata kamfen. Ba na son shiga cikin batutuwa da Peter Obi, wanda kuka san ba dan jam’iyyata ba ne. Amma na san ’yan APC masu biyayya ne ga APC.”