Tsohon shugaban jamâiyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya musanta cewa shi ne ya haddasa zanga-zangar da aka yi a jihar Edo.
Oshiomhole ya musanta hakan ne a matsayin martani ga kiran da gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya yi na kama shi kan zanga-zangar da aka yi a birnin Benin.
Tsohon gwamnan ya ce kiran a kama shi bai zama dole ba domin bai taba kiran zanga-zangar ba.
Karanta Wannan:Â Matakin Buhari ya yi daidai na dawo da amfani da 200 – Adamu Garba
Da yake magana ta bakin mai magana da yawunsa, Victor Oshioke, ya ce kawai ya roki mutanen jihar da su tsoratar da jamâiyyar PDP da yakin neman zabe ba tashin hankali ba.
Sanarwar da Oshioke ya fitar ta ce: âIdan Oshiomhole ya yi amfani da kalmar tsoratarwa, ya ce, su tsoratar da su da nasu kamfen, ya ce kada su bar filin Edo zuwa wasu jamâiyyu domin Edo jihar APC ce.
“Gajeren bidiyon yana ko’ina, idan suna da duka bidiyon bari su buga shi kuma suyi hukunci da gajeren wanda suke da shi, ya ce ya nuna? A’a.
âOshiomhole ya ce, su tsoratar da jamaâarsu, domin âyan jamâiyyar APC su iya tsoratar da âyan jamâiyyar da ke Edo.
“Oshiomhole bai yi wata magana da ke nuna cewa kowa ya tayar da kowa ba.”
Wasu matasa a jihar Edo sun tayar da tarzoma kan halin da ake ciki na Naira da kuma karancin man fetur a garin Benin.