fidelitybank

Ba ni ne na kashe Mohbad ba kuma ni ba dan kwaya ba ne – Naira Marley

Date:

Mawaƙin Najeriya, Azeez Fashola, wanda aka fi sani da Naira Marley ya sake jaddada iƙirarinsa na cewa ba shi da hannu a kisan tsohon abokin aikinsa, Ilerioluwa Aloba, wanda aka fi sani da Mohbad.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata da daddare, Naira Marley ya ce, kamar kowa, shi ma ya shiga cikin damuwa sosai sanadiyyar mutuwar tsohon yaron aikin nasa.

Naira Marley ya ce Mohbad ya bar kamfanin ‘Marlian Music’ ne a watan Satumban 2022, sai dai ya Ć™ara da cewa rashin jituwar da ke tsakaninsu ba ta kai yadda É—aya daga cikin su zai riĆ™a yi wa É—an’uwansa fatan mutuwa ba.

“Gaskiya ne cewa mun samu saÉ“anin fahimta a lokacin da muke aiki tare, amma saÉ“anin bai kai yadda mutane ke zuzutawa ba. Bai kai yadda za mu yi wa juna fatan mutuwa ba.” In ji Naira Marley.

Ya kuma ce sun riĆ™a Ć™oĆ™arin warware rashin jituwar ta hanyar shari’a gabanin mutuwar Mohbad.

Marley ya ce dalilin da ya sa ya yi gum da bakinsa game da mutuwar ta Mohbad shi ne saboda kaÉ—uwar da ya yi, da kuma gudun kada ya kawo cikas ga binciken da jami’an tsaro ke yi kan mutuwar.

Ya kuma ƙara da cewa ya bar Najeriya ne tun a ranar 31 ga watan Agusta, kuma bai dawo ba tun wancan lokacin, sai dai yanzu haka yana shirye-shiryen dawowa domin amsa gayyatar ƴan sanda.

‘Ni ba É—an Ć™waya ko Ć™ungiyar asiri ba ne’

Naira Marley ya kuma ce kamfaninsa ba cibiyar ta’ammuli da Ć™wayoyi ko Ć™ungiyar asiri ba ne. Inda ya ce shi kansa ba mai safarar Ć™waya ko É—an Ć™ungiyar asiri ba ne.

Ya ce “Marlian Music kamfani ne na wasu aminan juna, waÉ—anda ke gudanar da ayyukansu ta halastacciyar hanya. Manufarmu ita ce yin jagora ga mutane masu basira da tallafa musu.”

A ranar 12 ga watan Satumba ne Mohbad, mai shekaru 27 a duniya ya rasu, inda yanzu haka jami’an hukumar tsaro ta DSS ke gudanar da bincike kan mutuwar tasa.

Lamarin ya kai ga cewa an sake tono gawar mamacin bayan binne ta domin gudanar da bincike, inda yanzu haka ake jiran sakamako.

Mutuwar Mohbad ta haifar da ce-ce-ku-ce a Najeriya da ƙasashe maƙwafta, musamman a shafukan sada zumunta.

cnn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...
X whatsapp