Kocin Bayern Munich ya ce ba ya tsammanin shi kaɗai ne matsalar ƙungiyar, ya bayyana haka ne bayan sanarwar zai bar ƙungiyar a ƙarshen wannan kakar.
Tuchel mai shekara 50 zai bar ƙungiyar ne gabanin lokacin da aka cimma na yarjejeniyarsu.
“Abin da yake muhimmanci shi ne babu wani abu da aka yi shi a boye” in ji Tuchel da ya karɓi jagorancin ƙungiyar a watan Maris ɗin 2023.
“Yin abu abude na samar da ‘yanci, kuma abu ne mai kyau da ƙungiyar da ‘yan wasan haka kowa ma.”
Ya ƙara da cewa ‘yancin koci ne ya yi abin da yake so.
Kuma dole ya yi tunani kan abin da zai mai aiki na tsawon lokacin.