Babban kamfanin man fetur na ƙasa, NNPC ya ce, ba shi da masaniyar ɓatan N20bn daga lalitarsa ba.
Kakakin kamfanin, Garba Deen Muhammad cikin wata sanarwa ya ce kamfanin bai san da zaman zargin da kafar yaɗa labarai ta intanet, Sahara Reporters ta yi ba cewa kamfanin ya biya wasu masana na jabu N20bn.
Sanarwar ta ce “abin takaici ne da kafar yaɗa labaran ta yi wannan gagarumin zargi ba tare da duba illar yin hakan ba. Iƙirarin ɓatan N20bn ƙarya ce tsagwaran ta.”
Game kuma da iƙirarin da gwamnatin Ogun ta yi kan kuɗaɗen harajin da take bin hukumar ƙayyade farashin man fetur PPMC, NNPC ya ce PPMC ya ƙalubalanci iƙirarin.
Daga bisani kuma, gwamnatin Ogun ta miƙa batun kotu sai dai NNPC ya ce zai tabbatar da hujjojinsa.