Mutumin da ya fi kowa kuɗi a nahiyar Afirka, Aliko Ɗangote, ya bai wa jama’a da dama mamaki tun bayan da ya sanar da cewa ba shi da gida a ƙasashen waje.
Ɗangoto ya kuma sanar da cewa gidajensa biyu ne rak sannan kuma gidan haya yake sauka a duk lokacin da ya je Abuja.
Aliko Ɗangote ne dai attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirka kamar yadda mujallar Forbes ta fitar a karo na 13 a jere duk da irin ƙalubalen tattalin arziƙin da Najeriya ke fuskanta.
Dukiyar Ɗangote ta ƙaru da dala miliyan 400 a shekarar da ta gabata, inda yawan arziƙinsa ya kai dala biliyan 13.9 kamar yadda mujallar Forbes a lokacin.


