fidelitybank

Ba ni da alaƙa da masu fasa bututun jihar Rivers – Fubara

Date:

Gwamnan jihar Rivers da aka dakatar, Siminalaya Fubara ya musanta zargin da ake yaɗawa cewa, yana da alaƙa da ƙungiyoyin ƴanbindiga da ke fasa bututun mai, inda ya ce hotuna da bidiyo da ake yaɗawa ƙarya ne.

Ya ce ana yaɗa labaran na ƙaryar ne domin a tayar da zaune tsaye a jihar, sannan a ɓata masa suna, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

Fubara ya bayyana haka ne a wata sanarwa da sakataren yaɗa labaransa, Nelson Chukwudi ya fitar, inda ya ce Fubara na alla-wadai da yada labaran na farfaganda.

“Gwamna Fubara ba shi da wata alaƙa da ƙungiyoyin ƴanbindiga masu fasa bututun mai, kuma bai taɓa tunanin ƙulla wata alaƙa da su ba, sannan kuma ba zai taɓa alaƙa da ɓatagari da suke barazana ga zaman lafiya da tattalin arzikin jihar Rivers ba,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Fubara ya nanata shirinsa na tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa, inda ya ƙara da cewa ba a cin moriyar gwamnati ba tare da zaman lafiya ba.

www.punch news.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Tarzomar kama baƙin haure a Amurka na yamutsa hazo

An shiga rana ta uku a tarzomar da ake...

Alhazai sun kammala aikin Hajji bana

A ranar Lahadin da ta gabata ne alhazai miliyan...

Tinubu gyaran ƙasa za ka mayar da kai ba zaɓen 2027 ba – ACF

Ƙungiyar Tuntuɓar Juna ta Arewacin Najeriya, ta yi kira...

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...
X whatsapp