Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ce ba ya sha’awar zama ubangida ga kowane gwamna a jihar.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wajen wani taron karawa juna sani na inganta karfin aiki ga manyan jamiāan gwamnati a jihar Borno, ranar Litinin.
El-Rufai ya ce sau biyar kacal ya ziyarci Kaduna tun bayan da ya bar mulki kusan shekara guda da ta wuce.
āBa na son zama ubangida, shi ya sa ba na tsoma baki a abin da ke faruwa a Kaduna, ina son shi (gwamna) ya koya ya samu aikin da kansa.
āAbin da ba mu da shi shi ne shugabanci nagari, manyan abubuwan da ke tattare da ingantaccen shugabanci.
“Ya kamata shugaba ya samu mutanen kirki don samun aikin.
āAllah ne kadai zai iya yin komai da kanshi, komai girman kai a matsayinka na shugaba, za ka iya yin tasiri kamar mutanen da ke kusa da kai kuma shi ya sa ake cewa babu wata kasa da ta fi ingancin ayyukansa na gwamnati,ā inji shi.