fidelitybank

Ba na kwaɗayin kujerar Tinubu a 2027 – Yahaya Bello

Date:

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce ba ya sha’awar tsayawa takarar shugaban ƙasa domin fafatawa da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027 mai zuwa.

Yahaya Bello ya bayyana haka ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Michael Ohiare ya fitar, inda a ciki ya ce Yahaya Bello ya yi mamakin ganin wani faifan bidiyon da ake yaɗawa na yaƙin zaɓensa na 2022, amma ake cewa ya fara kamfe ne na zaɓen 2027 kamar yadda jaridun Najeriya suka ambato.

Sanarwar ta ce, “yayin da muke bayyanawa ƙarara cewa Yahaya Bello ba shi da burin takarar shugaban ƙasa a 2027, muna ƙara jaddada matsayarmu na goyon bayan sake zaɓar Tinubu a 2027”, in ji shi.

Mista Ohiare ya bayyana masu yaɗa labarin da ”masu yaɗa ƙarya”, waɗanda ba su da aikin yi sai ƙirƙirar ƙarya da yaɗa ta.

Yahaya Bello dai ya yi takarar shugabancin ƙasa 2023, kodayake ya daga baya ya janye a lokacin zaɓen fitar da gwani.

sun news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Har yanzu Tinubu bai nada Jakadun Najeriya ba – ADC

Jam’iyyar ADC ta soki yadda gwamnatin APC ta shugaba...

Har yanzu ina LP kuma ni ne zan iya saita Najeriya – Datti

Datti Baba-Ahmed, tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa a...

APC ta zama buhun kusa ta gaza a Najeriya – Amaechi

Tsohon gwamnan jihar Ribas, Chibuike Amaechi ya bayyana jam'iyyar...

An fara samun takun saka tsakanin Turkiyya da Najeriya a kan kungiyar Gulen

Kungiyar kare hakkin musulmi, MURIC, ta bukaci shugaban kasar...

Arziƙin Najeriya ya ƙaru da kashi 3.13 a farkon 2025 – NBS

Tattalin arzikin Najeriya ya ƙaru da kashi 3.13 cikin...

Kamfanonin lantarki za su katse wutar lantarki saboda bashi

Kamfanonin samar da wutar lantarki, sun ce suna iya...

Yunwa na kara tsananta a arewa maso gabashin Najeriya – ICRC

Kungiyar agaji ta Red cross (ICRC) ta bayyana yadda...

Ba zan taba watsawa Tinubu kasa a ido ba – IBB

Ɗan tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, wato...

Natasha kar ki kuskura ki dawo aiki – Majalisa

Majalisar Dattijai ta buƙaci Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta dakatar...

Za a yi ruwan sama da iska mai ƙarfi a jihohi harda Kano – NiMET

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMET) ta fitar...

Obi da El-Rufa’i za su koma jam’iyyar mu a hukumance – ADC

Sakataren yada labarai na rikon kwarya na jam’iyyar African...

Za mu tattauna da tarayyar Turai a kan Nukiliyarmu – Iran

Iran ta tabbatar cewa za ta gudanar da tattaunawa...
X whatsapp