Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa a shiyyar Arewa maso Yamma, Salihu Lukman, ya yi gargadi kan sauya tsohon shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Adamu da tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje.
Lukman ya yi gargadin cewa, maye gurbin Adamu da Ganduje zai zama kisan kai ga jam’iyya mai mulki. Ya yi magana a kan yadda rahotanni ke cewa Shugaba Bola Tinubu ya goyi bayan Ganduje ya zama shugaban jam’iyyar na kasa.
A karshen makon da ya gabata ne Adamu ya mika takardar murabus dinsa, kuma kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na kasa, NWC, ya tabbatar da hakan yayin taron da ta yi a ranar Litinin.
A wata sanarwa da ya sanyawa hannu, Lukman ya ce zaben Ganduje zai sabawa tsarin shiyyar da jam’iyya mai mulki ta yi. Ya jaddada bukatar yankin Arewa ta tsakiya ya samar da shugaban jam’iyyar APC na kasa bayan Adamu, inda ya kara da cewa NWC ta tashi tsaye ta jagoranci tattaunawar da za a yi.